JAWABIN GWAMNAN JIHAR BAUCHI STATE SENATOR BALA ABDULKADIR A LAUNCHING NA FORTUNE UNIVERSITY, JIBWIS NHQTRS JOS A GARIN MAGAMA GUMAU TORO LGA, BAUCHI STATE
Gwamna ya fara da bin matakan gaisuwa Kamar yadda yake tsarin taro.
Gwamna Bala ya anbace su daki-daki daga karshe ya bude Jawabin shi da cewa Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Sannan yayi salati ga Annabin Rahma.
Bayannan yayi godiya ga Allāh sannan ya roki Allah ya Karawa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir taimako. Sannan yace Filin da aka bayar yayi ne Haka don cigaban Addinin Allah.
Gwamna yace kungiyar Jibwis Nhqtrs Jos tana birge shi Dalili kuwa irin halin dattakun sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir. Yace Sheikh Malami ne Mai tawalu.
Gwamna yace yayi farin Ciki dajin Makarantun da Izala Nhqtr Jos take dashi da yawan dalibai har Wajen miliyon bakwai (7 million).
Ya yabi Izala Nhqtr Jos da iya tsari Wacce take birgeshi. Yace tsarin Jami'ar da akayi itama ta bashi shaawa ganin Master plan da Kuma bin ka'idodin doka kafin ma fara aikin Jami'ar.
Gwamna yayi fatan cewa Allāh yasa wannan Jami'a da za'a dabbaqa ta zama cibiyar bincike a duniya Baki daya.
Gwamna yayi Farin ciki da sunan Jami'ar Kuma ya kiraye mutan Toro da su godewa bisa wannan Jami'a da ka kawo Garin ko karamar hukumar Toro.
Gwamna cikin Jawabin shi yayi alkawarin Bada gudummawa wajen Ginin wannan Jami'a sannan ya kiraye dukkanin masu Hanu da shuni da su fitar da dukiyarsu don ganin Ginin wannan Jami'a.
Zaku iya sauki Application na a google play
👇👇👇
God bless you
ReplyDeleteAllah ya saka da alkhairi
ReplyDelete