JAWABIN RT. HONOURABLE IDRIS MAJE (DEPUTY SPEAKER NATIONAL ASSEMBLY, ABUJA) KUMA WAKILIN ALH AHMAD BOLA TINUBU A LAUNCHING NA FORTUNE UNIVERSITY, JIBWIS NHQTRS JOS A GARIN MAGAMA GUMAU TORO LGA, BAUCHI STATE
Ya fara da godiya ga Allāh, Sannan yabi matakan gaisuwa Kamar yadda yake a tsare.
Hon Maje ya anbaci cewar ya tsaya ne a matakin shi na daya daga Manyan Baki sannan Kuma a matsayin shi na wakilin Alh Ahmad Bola Tinubo (Dan Takaran kujeran Shugaban kasa a Jam'iyyar APC).
Hon Maje yace ilimi Shine ginshikin rayuwa Kuma shi na daya daga cikin daliban Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.
Sannan ya godewa Gwamnan Jihar Bauchi bisa bawa Izala Nhqtr Jos wannan Fili don Gina Jami'a.
Ya Kuma ambaci cewa Dan takaran kujeran Shugaban kasa a Jam'iyyar APC ya yarda da irin koyarwar da Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir yake yi.
A sa'ilin Jawabin shi dukkanin wakilan APC sun rufa mishi baya ciki Akwai Gwani, Hon Gagdi, Hon Babs, Barayan BAUCHI, Hon Aliyu Tilde, Former Minister Dan Burum.
Cikin Jawabin Hon Maje yayi bayanin cewa duk Wanda ya Raina Dan Arewa to yayi babban kure.
Alh Bola Tinubo ya Bada #120 Million Cewar Maje. Shi kuma Maje Ya bada #50 Million.
Kuma yayi alkawarin tattaro Yan Majalisar tarayya suzo su duba sauran ayyukan da za'a iya gabatarwa don bunkasa Makaranta.
Zaku iya sauki Application na a google play
👇👇👇