ZIYARA GA FHADILATUSH SHEIKH MUHAMMAD SANI YAHAYA JINGIR DAGA JAKADAN NIGERIA A KASAR RUSSIA (HIS EXCELLENCY, PROFESSOR ABDULLAHI SHEHU YIBAIKWAL) TARE DA KANINSA MAI GIRMA SARKIN NAMARAN ALH. ISA SHEHU SULEIMAN
02/06/1444H - 26/12/2022M
A safiyar yau ne Prof. Abdullahi Shehu Yibaikwal (Nigeria Ambassador to Russian Federation) tare da Kaninsa mai girma Sarkin Namaran Alh. Isa Shehu Suleiman sun ziyarci jagoran sunnah na Africa, shugaban majalisar malamai na Kasa da kasa Fhadilatush Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir bisa jagorancin shugaban majalisar malamai na Jihar Pilato Dr. Hassan Abubakar Dikko da kungiyar Jibwis Kanam Nhqrs Jos karkashin jagorancin Ustaz Abdullahi Hassan Tukur (Jarman Jhar).
Jakadan wanda ya yaba wa Sheikh bisa irin kokarin da yake gabatarwa wajen wa'azi da cigaban addini da ma kasa baki ɗaya, Prof. Yace Sheikh mutum ne da Allah ya cire wa kwaɗayi da gudun duniya. Sannan ya mika wa Sheikh kyauta na musamman.
Sheikh Jingir yayi godiya sannan yace wannan ziyara ta kasance abun farin ciki gare shi.