GANIN IDO BA YA HANA CIN KAI: KIRA NA MUSAMMAN DON CETO AL'UMAR ATAFOWA
Da sunan Allah Mai Rahma, Mai jinkai.
A bayyane take cewa Mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, Kauran Bauchi kuma Jagaban Katagum, Shugaba ne da ya zo da kishin ciyar da wannan Jiha tamu ta Bauchi gaba, lura da ayyukan alheri masu matukar muhimmanci da tasiri ga rayuwar al'uma da ya sa a gaba a dukkan fadin Jihar Bauchi lungu da sako.
Hakazalika, idan za a yi magana ta gaskiya, mu al'umar Karamar Hukumar Itas-Gadau mun yi matukar dace da samun ayyukan Maigirma Gwamna a dukkan fannoni rayuwa, muhimmi daga ciki hanyar Itas zuwa Gadau da aka kirkire ta sabuwa fil mai tsawon kilomita 25. Dole ne mu yi wa Maigirma Gwamna godiya da jinjina don wannan ba-zata da ya yi mana na kokarin hade manyan biranenmu biyu.
A wata ziyarar gani-da-ido da na kai a watan Yunin wannan shekara na ga yadda ake kan aiki babu kama-hannun-yaro, musamman kafa manyan turakun dora gada ta zamani a kan babban kogin da ya ratsa inda hanyar za ta bi, kamar yadda kuke gani a hotunan da ke kasa, a yayin da aikin shara da zuba birji kuwa tuni ya hade garuruwan namu biyu. Tabbas wannan aiki ne da yake lakume dimbin miliyoyin kudaden Jihar mu da muke fatan kwalliya ta biya kudin sabulun su.
Sai dai, kamar yadda masu magana ke cewa ganin ido ba ya hana cin kai, ya zama dole mu yi kira na musamman ga Maigirma Kauran Bauchi kuma Jagaban Katagum da ya yi wa Allah ya kalli halin da al'umar yankin kasar Zubuki suke ciki, musamman babban birnin wannan yanki wato garin Atafowa.
Wannan babban gari mai dimbin albarkar yawan jama'a dai duka-duka nisan sa da Shalkwatar Karamar Hukumar wato Itas bai wuce nisan kilomita 15 ba. Yanki ne da ya hada al'uma dunkulalliya mai kishin cigaban Jihar Bauchi da Karamar Hukumar Itas-Gadau ta fuskar bayar da gudummawa wajen zaman lafiya da harkokin ilimi da sana'a, musamman noma da kiwo da fatauci da kuma sauran harkokin kasuwanci.
Wannan gari a halin yanzu ya zamo tamkar wani
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM