DABI'AR RUBUTU JIKIN RIGA YAYIN KAMMALA JAMI'A KO KOLEJI DA KUMA SAKANDIRE HANYAR NUNA GODIYA NE KO KUMA WATA KIRKIRARREN DABI'A CE WANDA TA SABAWA MUSULUNCI DA URFIN MUTANEN AREWA
✍️ Ukasha Koko Abu Shuraim
Muna wani lokaci da wai dalibi ko daliba da zaran sun kammala Jarrabawar karshe na kammala karatunsu sai kaga sun Sanya T-shirt ga Yan Manyan makarantu, su Kuma Yan sakandire a jikin uniform kowa Yasa musu hannu a jikin rigar ko uniform din da sunan sign out.
Abinda zai Kara baka mamaki shine yanzu har yaran da suka kammala karatun sakandare suma sun mayar dashi dabi'a wacce har in sunsan ba za'a bari suyi ba wasu daliban har canza makaranta suke zuwa ga wacce za'a bari suyi.
Wannan dabi'u dai sun sabawa tsarin nuna Farin ciki da Shari'a ta gindaya kuma haka al'adarmu managarta basu lamincewa irin wannan dabi'un ba.
Abin mamaki wannan dabi'a a yanzu ya mamaye dukkanin Jami'o'i da kwalejojin da Makarantun sakandire a Arewa wacce a baya hakan bata faruwa. Wani Abin takaici ma harda Daliban da sukayi karatu fannin Islamic Studies da Arabiyya, za kaga suma sun zamo Yan Abi yarima asha kida.
Jami'o'i a Arewa da manyqn kwalijoji sun fara haramta irin wannan dabi'ar bayan kammala karatu. Jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Katsina da Kuma Kwalejin ilimi na Jigawa dake Gumel sun fitar da Bayanin haramtawa dalibai wannan dabi'ar domin ta fara wuce Gona da iri.
Daga karshe Ina bawa sauran Jami'o'i da suyi koyi da Jama'ar Umaru Musa Yar'adua da Kuma Kwalejin ilimi dake Gumel wajen Sanya takunkumi ga dalibai.
Sannan Ina Kira ga Shugabanin Makarantun sakandare su sa ido sosai domin Abin ya fara wuce gona da iri Wacce wasu daliban har "HIKE OUT" suke shiryawa a wajen gari Maza da mata tare da yin batala iri-iri wai da sunan murnar kammala sakadare alhali suna da tafiya Mai nisa gabansu.
Babu laifi nuna Farin ciki yayin kammala karatu. A musulunci akwai Tsari Mafi kyau wajen nuna Farin ciki. Godiya ga Allah bisa ni'ima ibadane Amma bisa bin salon da shari'a ta yarda da shi. Don haka dalibai abi tsarin Allāh don samun Nasara cikin dukkanin lamura.
Annabi ya ce: BABU WANI BAWA WANDA ZAI FARO WANI ABU MAI KYAU, IDAN AN BISHI A KANSA, FACE YA NA SAMUN LADAR WADANDA SU KA BI SHI (HAR ABADA). [Muslim; 1017]