Rohotonnin wasu daga Cikin ayyukan kungiyar JIBWIS NHQ JOS a wasu sassan jihohin Nigeria.
Fitowa ta 30th.
Daga Alqassem Muhammad Ardobijaji
#Jihar_Filato
Asheikh Muhammad Sani Yahaya Jingre Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa na JIBWIS NHQ JOS ,Ya karbi Baquncin Shugaban Rundunar STF a headquarter Kungiyar dake Jihar plateau Jos.
Kuma wannan ziyarace don ya gabatar da kanshi ga Asheikh tare kuma da neman Sheikh din ya mishi addu'ah kan aikin da aka dora mishi na jagoranci, a karshe Sheikh yayi addu'ah tare da nasiha.
An gabatar da mitin da wa'azin Jihar a MANGU.
An gabatar da taron wata wata na Karamar hukuma Jos ta Arewa.
#Niger_Republic
Jakadun alheri na kungiyar JIBWIS NHQ JOS a matakin ta na Kasa da Kasa ta tura wakilanta zuwa kasar Niger domin gabatar da ayyukan addini.
#Jihar_Gombe.
An gabatar da mitin da wa'azin Jihar Gombe a garin REME
Shugaban Majalisar malamai na Jihar Gombe ya jagoranci bude masallacin Jumma'a a garin KEMBU.
Rundunan Agajin Gundumar BIWA sun gabatar da mitin a garin WAWA.
Ana cigaba da gabatar da wazuzzukan mako mako a fadin jihar Gombe.
#Jihar_Niger
Al'umman Jihar Niger karkacin shugaban Majalisar malamai na Jihar Niger Sheikh Abubakar Abu Sumayya Minna sun ziyarshi Sheikh M. Jingir a ofishin sa dake Jos shelkwatan kungiyar JIBWIS.
#Jihar_Bauchi.
Kungiyar Jibwis Karamar hukumar DARAZO ta sayi sababbin mitoci guda biyu dan aikin addinin Allah.
Kwamitin matasa reshen Karamar hukumar Bauchi sun gabatar da MUHADARA a Bauchi.
An kaddamar da gidauniyar neman taimako a Bauchi, dan sabanta makarantar School for Higher Islamic Studies BAKARO da kuma sayan motar makarantar domin zirga zirgan hukumar makarantar.
#Jihar_Zamfara
Dan takarar gwamna a jam,iyyar PDP Dr. Dauda Lawal Dare ya gwangwaje Ustaz Umar Hassan Gusau (Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na jihar zamfara na 1) da sabuwar mota kirar Camry
Ana cigaba da gudanar da wa,azin unguwannin a garin T/mafara, Gusau da yankin Gummi.
An gabatar da mitin na Kwamitin social media reshen T/mafara.
#Jihar_Kebbi
Sheikh Abdurrahman Isah Jega ya gabatar da shiri na musamman a tashar KBTV akan RAYUWAR ADDINI.
Ana cigaba da gabatar da TALIMAT na littatafa daban daban a sassan jihar Kebbi.
#Jihar_Benue.
A matakin ta na jiha an gabatar da wa'azin mako mako a Cikin garin MAKURDI.
#Jihar_Kano
Sheikh Dr Sani Shareef Bichi ya gabatar da Muhadara mai taken Bidi'ar Mauludi da Da'awar ganin Annabi bayan wafatinsa.
Ana cigaba da gabatar da TALIMAT daban daban a sassan Jihar.
An gabatar aikin gayyar yankan shinkafar gonan kungiyar JIBWIS NHQ JOS reshen Beta.
#Jihar_Yobe
Kwamitin matasa reshen DAMATURU sun gabatar da MUHADARA.
Sheikh Dr Musa Salihu Alburhan ya gabatar da gagarumin wa'azi a garin Potiskum.
Ana cigaba da gabatar da wa'azuzzukan mako mako a sassan jihar irin su Gaidam da sauran su.
#Jihar_Borno
An gabatar da wa'azin mako mako anan Cikin Maiduguri Karkashin Jagorancin Shugaban Majalisar Malamai JIBWIS BORNO, Sheikh Modu Mustapha Albarnawy.
Wa'azin Yana Gudane anan Masallacin Izala Dake Bulumkutu.
Malami Na Farko Mal Yunus Mustapha
Na Biyu Ustaz Dr Ali Waziri Shugaban Kwamitin Wa'azin Matasa Na Jihar Borno
Malami Na uku Sheikh Bar Ahmed Abdulkadir Legal Adviser JIBWIS BORNO
Malami Na Hudu Kuma Na Karshe Shugaban Majalisar Malamai JIBWIS NHQ JOS BORNO State, Sheikh Modu Mustapha Albarnawy
Sheikh Zakariya Modu Mataimakin Shugaban Malamai JIBWIS NHQ JOS BORNO State, Shi Ya Rufe Wa'azin da Adu'a
Jihar_Nasarawa
Ana cigaba da gabatar da wa'azin mako mako da kuma TALIMAT daban daban a sassan jihar.
#Jihar_Adamawa_Jigawa_Taraba_Kogi_Jigawa_Kaduna ana cigaba da gabatar wa'azin mako mako da TALIMAT a sassan jihohin.
#Jihar_Katsina
An gabatar da mitin na kwamitin wa'azin matasa na karamar hukumar Katsina.
An gabatar dashen itatuwa a masallatan Jibwis karkashin jagorancin shugaban malamai na Jihar.
#Jihar_Sokoto
Rundunan Agajin Jihar Sokoto sun gabatar da mitin a Cikin garin Sokoto.
Kwamitin wa'azin matasa na Tambuwal Local Government sun gabatar da mitin.
#FCT_Abuja
Innalillahi Wainna ilaihirrajiun
Allah ka Jikan shugaban Majalisar gudanarwa na FCT.
WAKILAN SHUGABAN MALAMAI NA KASA SUN GABATAR DA TA"AZIYAR SHUGABAN KUNGIYA NA FCT ABUJA,
Wakilan Fadilatul Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Shugaban Malamai na kasa da kasa Sun isar da sakon Sheikh din tare da gabatar da ta"aziya ga Sashin Shuwagabannin fct Abuja da Yan Uwan da iyalan marii gayi Shugaban Kungiya na Abuja Alh Yunusa Aliyu Allah ya jikan shi da Rahama , wakilan Sheikh Sune
Al-Hafiz Aliyu Abdulwahab Matai Makin Shugaban malamai na Jahar Filato tare da Imam Jafar Husaini Shugaban makarantar nazari Addinin musulunci mai zurfi takasa Kuma babba limamin masallacin Juma"ah na yantaya Jos, da Ustaz Muhammad Rabiyu musa Director Jahar Filato da Alh Aminu Abubakar P.A da Alh Abubakar Jibrin State Intelligent office na Jahar Filato da Hafiz Auwal musa Hassan da Malam kabiru Haruna.
Muna Mika godiyarmu ga wakilammu na jihohi tareda wakilan mu FCT ABUJA.
Alqassem Muhammad Ardobijaji
MD/CEO #IzalaAmakonJiya
26/9/22