Rohotonnin wasu daga cikin ayyukan kungiyar JIBWIS NHQ JOS a wasu sassan jihohin Nigeria a makon data gabata.
Fitowa ta 29.
Daga Alqassem Muhammad Ardobijaji.
#Jihar_Filato
Shaikh Muhammad Sani Yahya Jingir Shugaban Malamai na kasa da kasa ya gabatar da MOTOCIN Njange Ndure guda biyu Wanda aka gabatar da gidauniya a watan da yawuce a garin magamar Gumau dake jahar Bauchi
Sheikh Jingir yayi Addu'ah tare da Yabawa Ardo mamud tare da fatan Alkairi Allah yasaka da alheri.
#Jihar_Gombe
Ash Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya amsa gayyatar da Gomnan jihar Gombe ya masa domin halartan Daurin auren Dan Gomnan jihar Gombe.
Rundunan Agajin Dukku sun gabatar da Workshop wa "yan Agaji.
Rundunan Agajin FUNAKAYE, NAFADA, RABADU da BIWA, sun gabatar da zornal mitin a BIRIN FULANI.
#Jihar_Kaduna
Karamar hukumar LERE sun gabatar da mitin a garin GARUN GURAMA.
Jibwis nhq Jos Zaria ta gabatar da lecture a cikin ABU Zaria biyo bayan gayyatar MSN suka musu.
#Jihar_Katsina
Wakilan Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Wanda suka hada da Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi, Sheikh Aliyu Rasheed Makarfi tareda mai masaukin su shugaban Majalisar malamai na Jihar Sheikh Sulei Agaji sun gabatar da gagarumin wa'azi a cikin garin Katsina.
#Jihar_Nasarawa
An gabatar da wa'azin Jihar Nasarawa a cikin garin Keffi.
#Jihar_Zamfara
Kwamitin Media na Jihar Zamfara (JIBWIS INTERNET MEDIA COMMITTEE ZAMFARA STATE CHAPTER) sun gabatar da meeting na jiha a garin Gusau
Ana cigaba da gudanar da wa,azin sati-sati a garuruwan T/mafara da Gusau da sauran sassan jihar
#Jihar_Lagos
An gabatar da wa'azin Jihar Lagos a IKEJA
#Jihar_Borno
GWAMNA ZULUM YA DAURA MATAKI NA KASO 75 CIKIN 100 NA ALƘAWARIN DA YA DAUKA DON KAMMALA MASALLACIN IZALA A BIU.
Cikin kokari da Mai girma Gwamnan jahar Borno Prof. Babagana Umara Zulum yakeyi tare da Mataimakinsa H.E Umar Usman Kadafur, don ganin sun kammala Masallacin Izala na daya dake kan titin Maiduguri Arewa da Shataletalen tsakiyar gari anan cikin garin Biu;
A yanzu haka an gama fentin ko ina da ko ina ciki da wajen masallaci dama azuzuwan dake saman masallaci,
Sannan an sanya wutan lantarki da fanka a cikin masallacin, ankuma hada dukkan wata na'ura na cikin masallacin, mu samman mai daukan sauti ya kai nesa,
A halinda ake ciki yanzu; abubuwan da suka rage basu da yawa wanda basu wuce kaso 25 cikin dari, muna kuma fatan gwamna zai gama cika alkawarin sa kamar yadda ya fara, Allah kuma ya saka musu da Alkhairi, Amin!
#Jihar_Bauchi
An gabatar da wa'azin hadin Gwuiwa tsakanin CHINADE LGA/MADARA LGA garin LARISKI.
Kwamitin matasa sun gabatar da wa'azin raya karkara a garin JUMBERI dake gundumar MADARA
#Jihar_Kano
An gabatar da wa'azin hadin Gwuiwa tsakanin BURRA, GARKO LGA, TAKAI LGA, ALBASU LGA DA KIBIYA LGA, a garin MAGAMI
Ana cigaba da gabatar da talimat a sassan jihar.
#Jihar_Kebbi
A Cikin wannan satin ne Kwamitin Maaikata Lafiya na Wannan Kungiyar na Jihar Kebbi ( JIBHAN KEBBI STATE) Sun kafa Kwamitin a Karamar hukumar Mulki ta Zuru Inda aka Bada shugabanci na rikon kwarya
An hasko makaranta horas da malamai wato JIBWIS COLLEGE OF EDUCATION JEGA ta dau harama ana cigaba da Mata kolliya.
Sheikh Abdurrahman Isah Jega da sauran maluma suna cigaba da gabatar da talimat.
#Jihar_Benue
Kwamitin matasa na jihar sun gabarta da taro a Makurdi.
An gabatar da wa'azin na karamar hukumar Makurdi
#Jihar_Taraba
An gabatar da MUHADARA a Wukari
#Jihar_Niger
Shugaban Majalisar malamai na Jihar Sheikh Hafiz Abubakar Abu Sumayya ya halarci taron bita na kungiyar limamai na Jihar Niger.
#FCT_Abuja
Ash Sheikh Yusuf Sambo ya gabatar da gagarumin wa'azi a Jibwis Islamic center Guzafe
Jihohin Yobe, Sokoto, Kogi,Niger, Adamawa etc ana cigaba da gabatar da Talimat da wazuzzukan mako.
Muna Mika godiyarmu ga abokan aiki na Jibwis nhq Jos Kuje FCT Abuja tareda wakilan mu na jihohi.
Alqassem Muhammad Ardobijaji
MD/CEO #IzalaAmakonjiya
19/9/22.
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM