Rohotonnin wasu daga cikin ayyukan kungiyar JIBWIS NHQ JOS a wasu sassan jihohin Nigeria a makon data gabata.
Fitowa ta 28.
Daga Alqassem Muhammad Ardobijaji.
#Jihar_Filato.
Allah ya kaddari Sheik Muhammad Sani Yahya dawowa Nigeria bayan tsawon kwanaki da yayi a Kasar Saudi Arabia dan gabatar da aikin Umrah.
Rundunan Agajin Jihar Filato sun sauka a Karamar hukumar Riyom dan gabatar da aiki na musamman.
#Jihar_Adamawa
An gabatar da wa'azin jiha a garin Mayo Belwa.
#Jihar_Gombe.
Kwamitin matasa na Jihar Gombe sun gabatar da muhadara a garin Kumo.
Kwamitin matasa reshen kwami LGA sun gabatar da muhadara a Bojude.
Wakilan kungiyar JIBWIS NHQ JOS reshen Biwa sunyi ganawa na musamman da shugaban Majalisar malamai na Jihar Gombe.
#Jihar_Zamfara
Sheikh Abdul-lahi Umar Dalla Dallah (Shugaban Majalisar Malamai na jihar zamfara JIBWIS NHQ JOS) ya gabatarda wa,azin Mako-mako wanda gwamnatin jihar zamfara ke shiryawa duk sati
Wa,azin ya samu halartar kwamishinoni, Masu bada shawara, manyan sakatarorin gwamnati da masu martaba Sarkin katsinan Gusau da Sarkin Maru (Emir of Gusau&Maru)
Kwamitin matasa reshen TAFARA MAFARA sun gabatar da Muhadara
#Jihar_Yobe
First Aid Group of JIBWIS Damaturu Division Tafara gudanarda Division Camping Rawar Dajin Yan Agajinta Dan zaburar dasu Akan aikinsu da karamusu Ilimi akan aiki DAMATURU DIVISION CAMPING 2022
Allah yabamu nasara.
#Jihat_Bauchi
Kwamitin matasa reshen jihar Bauchi sun gabatar da mitin da Muhadara a garin Faggo.
#Jihar_Katsina
Muna Mika Taziyyarmu ga mutanen Bokari bisa rasuwan daga cikin shugabanninsu.
#Jihar_Benue
An gabatar da wa'azin Karamar hukumar makurdi
Jihar_Kebbi
Sheikh Abdullrahman Isah Jega ya sauka garin GULMA a Karamar hukumar Argungu.
Kwamitin matasa reshen jihar sun gabatar da wa'azi a garin Naman Goma.
#Jihar_Niger
Shugaban Majalisar malamai na Jihar ya Kai ziyaran aiki na musamman wajen Sheikh Abdullrahman Isah Jega.
#Jihar_Borno
HON MUKTARI BETARA ALIYU YA DASA TUBALIN GININ MAKARANTAR GABA DA FIRAMARE A GARIN KWAYA KUSAR. Karkashin Kungiyar Jibwis Nhqtr Jos.
Kungiyar Jibwis Nhqtr Jos, Rassan Kananan hukumomi hudu Wadda Suka hada Da Bayo,Hawul, Kwaya Kusar Da Shani.
Kungiyar Ta Dasa Tubalin Gini Makarantar a Yau a Garin Kwaya, Wadda Ta Gaiyaci Rt. Hon Muktari Betara Aliyu, Dan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Mazabar Bayo,Biu, Kwaya Da Shani. Domin Ya Kaddamar da Dasa Tubalin.
Hon Betara, Yasamu Wakilcin, Hon Salihu Adamu Yanga, Mai Bada Shawara na Mussaman Ga Mai Girma Gwamanan jihar Borno, Daga Cikin Shuwagabani Akwai, Shugaba Majalisar Mallamai Na Kwaya Kusar, Kuma Shugaba Committee Makarantar, da Sauran Shuwagabani Kungiyar,Masu Ruwa da tsaki na Garin Kwaya da mahalarta taro.
Yayin Jawabin shi, Hon Yanga, Ya Yabawa Wannan Kungiyar Ganin yadda take aiki don Cigaban Addinin Musulunci, ya Kuma yi bayanin Cewa Insha Allah, Ashirye Yake Shida maigida shi Domin Tallafawa Wannan Makarantar a kowani lokaci
#Jihar_Lagos
Musulunci ya samu qaruwa yau wani Igbo ya musulunta a masallacinmu na Jumu'ah dake pipe line Gatan Kowa Alimosho local government Lagos State
#Jihar_Kaduna
Kwamitin matasa reshen jihar sun gabatar da muhadara a Kaduna.
#FCT_Abuja
ZIYARAR GANI DA IDO (TUWA) NA F.C.T ABUJA, KUJE AREA CANCEL
An gabatar da wasu ziyara harda sarakunan mu na kuje da yan siyasa . karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Ibrahim Daguri
SHUGABAN MALAMAI NA F.C.T ABUJA DA SAURAN MATAIMAKA.
Sheikh Abdullahi Abdulrahman MATAIMAKIN SHUGABAN GUDANARWA NA FCT ABUJA DA SAURAN MATAIMAKA
Umar Sani Fofure DAREKTAN AGAJI NA F.C.T DA SAURAN MATAIMAKA.
DA YAN KOMITIN NA F.C.T ABUJA
Muna godiya ga wakilammu.
Alqassem Muhammad Ardobijaji
MD/CEO #IzalaAmakonJiya
12/8/22
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM