LIMAMIN LIMAMAI NA AHLISSUNNAN JIHAR SOKOTO, IMAM ABUBAKAR USMAN MABERA.
Idan kana so kasan me ake kira Kamun Kai, menene Natsuwa, me ake nufi da Tawadhi'u, da zaran kaga Babban Limamin Masallacin Mallam Buhari Dan Shehu Usmanu Mujaddadi dake Birnin Sokoto, kuma Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar IZALA JOS, Imam Abubakar Usman Mabera, ba sai kayi tambaya ba, zaka gamsu da shine.
Sheikh Imam Abubakar Usman Mabera baya zuwa Garkar kowane dan Siyasa dake Jihar Sokoto sai idan an gayyace shi. Koda dan Siyasa ya nemi saduwa da Malam shi kadai, bai taba yarda da haka, sai ya tara 'Yan Majalisarsa na Koli, idan zaka ganshi to ka ganshi gabansu, don kariyar mutuncin kansa. Malam ya karantar damu wannan Tarbiyya mai cike da kamun kai da yin Tawakkali ga AllaH (SWT). Ya fada muna cewa koda mutum na zaune a karkashin Kasa Rabonsa zai iskammai, kuma koda ya shiga har cikin dakin dan Siyasa idan babu rabonsa haka zai fito busashshe. "Muna nan Biye".
Imam Mabera mai Hakuri ne, mai Tausayi da Taimako da watsa Kyaututtuka ga mabukata, don yin koyi da Manzon AllaH (saw). Matsayinsa Shugaban Addini shaida ne ga kowane mutum daga kowace Karamar Hukumar Mulki 23 dake cikin Jihar Sokoto, babu inda za'a gayyaci Malam Daurin Auren kowanene sai ya tafi, idan akayi rasuwa komai nesan wuri daga Sokoto, lokacin da zamuji labari ya isa wajen ya sallaci wannan Gawar ya dawo. Gameda tafiye-tafiyen da yakeyi irin wadannan, ya zama dole mu dauki matakin taka masa Burki, saboda yanayin Tsaro.
ALLAH YA KARA WA SHEIKH IMAM ABUBAKAR USMAN MABERA LAFIYA DA NISAN KWANA MASU ALBARKA, TARE DA 'YAN MAJALISARSA BAKI DAYA.