Asabar.. DADIN KOWA
Lahadi.. KWANA CHASA'IN
Litinin.. LABARINA..
Talata.. MAIMAICIN LABARINA da MAIMAICIN DADIN KOWA..
Laraba.. MAIMAICIN KWANA CHASA'IN..
Alhamis.. GIDAN BADAMASI..
Jum'at.. ZAIRA..
Gaba daya an lalata ma kwanakin dake cikin sati a banza da wofi.. kullum jira kake sabo ya fito.
..Shin kai Wacce Rana Ka ajiye domin koyon.. Al Qur'an Mai girma...???
Wace Rana Ka ajiye domin koyon.. HADISIN Annabi Muhammad (S.A.W)???.
.Wace Rana Ka ajiye domin koyon.. FIQHU..???
Wace Rana Ka ajiye domin koyon.. SALLAH..da sauran ayyukan Addini...Ya kai dan Uwana..???
Ko kuma kana tinanin 'yar Islamiyyar da kaje a wasu 'yan shekaru ta isheka?
Shin kana nufin kasan komai a fannin Addininka?
Shin kana nufin kasan komai ahukunce-hukuncen Ibadarka?
Littafin sanin ibada guda nawa ka karanta guda nawa ka haddace?
Shin anya kuwa ka haddace AlQur'ani kamar yarda labaran wannan shirye-shirye suka zauna akanka?
Shin ka san sunan Sahabban Annabi kamar yarda ka san sunan dukkanin 'yan wasan fina-finan nan?
Awa daya zuwa awa biyu ka ke ba dukkanin shirye shiryen nan, shin awa nawa ka ke ba bautar Allah a kowace rana ?
Awa nawa kake warewa domin yin Addu'a akan lamarin rayuwarka?
Shin anya kuwa munaso muga dai dai ?
Anya kuwa yahudawa ba suyi nasara ba akanmu ?
Anya haka ya dace dukkanin 'ya 'yan Musulmi su kasance ?
To gyara kayanka dai ba zai zama sauke muraba ba
Muyi hattara jama'ar Musulmi
Idan kunne ya ji jiki ya tsira
Ya ubangiji ka tsare mana i'manin mu kaji kan maga batanmu