HUKUNCIN BIDI'O'IN AURE A MUSULUNCI
Bayani daga zauren Fiqhu tare da Karin sharhi daga Dalibi Ibrahim Maina Muhammad
Assalamu alaikum: Bayan godiya ga Allāh da salati ga Manzon tsira (saw).
Lallai ne mutanen wannan zamani wasu cikin su sunyi nisa wajen tsunduma cikin bidio'i yayin bikin aure.
An baro hakikanin yadda ake bikin aure bisa koyawar Annabi (saw) an koma koyi da yahudu cikin kulla aure. Irin Munanan bidi'o'in da ake yi Abin takaici ne matuqar gaske.
Abin mamaki har da masu iqrarin su Ahlus Sunna ne Amma bukukuwa gidansu Gwamna bikin wani Wanda ma Bai taba misalta kanshi da Sunna ba.
Wani ya zamo ya barwa mata ragamar komai game da auren YA'YANSHI Kai wasu ma idan har a aurensu Wanda zasu aura baya da ra'ayin irin wadannan shiriritan to sun gwammaci a fasa auren.
To ku Yan koyi da yahudu yayin sure saurara kuji abunda shari'a yace:
Shaikh Dr Muhammad Bakru Isma'eel acikin littafinsa mai suna Fiqhus Sunnah, juzu'i na biyu shafi na 37 yana cewa "Duk da cewar shari'ah mai hikima (wato shari'ar musulunci) bata ajiye wani iyaka game da Qankantar sadaqi ko Qurewar yawansa ba, to amma ba'a son zurfafawa acikinsa saboda cikin yin hkaan akwai tsanantawa da takurawa. Domin tsanantawa cikin sadaqi (:ko dukiyar aure) shike sanya samari suna kauda kansu daga yin aure, kuma wannan shi ke haifar da abubuwan barna wadanda ba boyayyu ba, game da lalacewar dabi'a da zamantakewar jama'a".
Duk da cewar shi Malamin yana magana ne ka'dai game da tsadar sadaqi, to amma mu anan Qasar hausa bayan tsadar sadaqin ma akwai wasu miyagun bidi'o'in da mutane suka Qirkiro suka dora ma kansu, wadanda harma anfi tsanantawa akansu fiye da shi kansa sadaqin ma.
Daga cikin abubuwan da zan iya tunawa ana yinsu anan Qasar hausa game da bidi'o'in aure akwai :
1. Kayan "Na-gani-inaso".
2. Kudin Tambayar arziki.
3. Kayan Sa-rana.
4. Kudin Mijin-baya (wanda ake bama 'ya'yan kawunnan amaryar).
5. Kudin Uwar Amarya.
6. Kudin Sa-lallen Amarya.
7. Sa lallen Ango.
8. Party, Picnic, etc.
9. Fulani day.
10. Kauyawa day.
11. Arabian Night. I
12. Rawar kalangu.
13. Chakuduwar Maza da Mata.
14. Kudin sayen bakin amarya.
Wadannan ka'dan ne na zakulo. Koda ba'a yin wasu daga cikinsu ayankin da kake rayuwa, to awasu yankunan duk ana yi, ko fiye da haka ma.
Wadannan abubuwan duk sun sa'ba ma sunnar Annabi Muhammadu ﷺ, wanda Shi Allah ya aiko mana kuma yace mu kwaikwayi aikinsa. Tabbas hakika Manzon Allah ﷺ yayi aurarraki da dama, kuma shima ya aurar da dukkan 'ya'yansa mata. Amma ba'a ruwaito cewa an ta'ba aikata koda guda daya cikin wadannan abubuwan alokacin bikinsu ba.
Lokacin da ya auri Nana A'isha wasu mata ne 'yan tsiraru suka rakota, kuma ba'a yi wani biki ko kade-kade ba, ballantana chakudar maza da mata. Haka kuma lokacin da ya aurar da 'yarsa Fatimah wacce ita ce Shugabar dukkan matayen duniya da lahira amma ba'a yi biki ko rawa ko shagali ba.
Imamu Ahmad bn Hanbal ya karbo ta hanyar Nana A'isha (Allah ya yarda da ita) tace Manzon Allah ﷺ yace *"Hakika auren da yafi albarka shine wanda dawainiyarsa tafi sauki"*
Awani hadisin kuma yace *"Albarkar mace shine : Saukin sadaqinta, da saukin dawainiyar aurenta, da kyawun halayenta.*
*"Shu'umancin mace kuma yana cikin : Tsadar sadaqinta, Wuyar dawainiyar aurenta, da kuma munin halinta"*
Shaikh Muhammad Bakru Isma'eel yace "Da yawa daga cikkn mutane sun jahilci wannan sanarwar ta Manzon Allah ﷺ shi yasa suke kauce mata suke bin hanyoyi irin na zamanin jahiliyyah cikin zurfafa sadaqi (ko dawainiyar aure) suna la'akari da Qarairayin abubuwa bayyanannu.
Sai kaga mutum yana Qin aurar da 'yarsa ga wani mutum komai matsayin ilimin mutumin ko mutuncinsa ko rikon addininsa. Sai dai (in sunga alamar cewa) mutumin zai iya biyan sadaqi mai yawa, basu damu da halin mutumin ba.... Sai kace ita yarinyar da za'a aurar din ta zama wata kadara ce za'a saye ko sayarwa".
Shehu Usmanu 'dan Fodio acikin littafinsa IHYA'US SUNNAH (shafi na 123) da yazo yin bayanin bidi'o'in shaidanci da mutane suka kirkiro acikin lamarin aure sai yace "Yana daga cikin wannan (bidi'o'in) irin bikin walimar dake ha'de da 'Barna kala-kala (kamar chashe rawa ko chudanyar maza da mata) wannan bidi'ah ce muharramah bisa ra'ayin dukkan malamai.
Shehu yace "yazo acikin sharhin ALMUFIDAH : Babu kokwanto cikin haramcin wannan da kuma muninsa". Muna neman tsarin Allah daga bacewa da tabewa.
Yaci gaba da cewa "Zaka ga mutum (Allah ka tsaremu da sa'bonka da rashin kishin iyali) kaga mutum wai farkon abinda zai bude dashi cikin aurensa kuma ya gina auren nasa akai shine wannan fasadin mai girma. Wanda duk mutum dake da kwayar zarrah na kishin musulunci bazai yarda da haka ba. Balle kuma wanda keda rikon addini koda Qankani ne.
Zaka ga mutum ya tara jama'a ya girmamasu (wato ya basu wuraren zama da abinci) sannan mataye daga dangin Mijin suyi ado suyi kwalliya su fito su hadu da wadannan jama'ar da ya tara, sannan mutane su tattaru daga kowacce nahiya".
Sannan yace "Babu shakka duk bikin auren da ya zamto bisa wannan tsarin aka yishi, to babu albarka cikinsa kuma babu alkhairi. Kaichon shi kansa Mijin (wato angon) da kuma duk wadanda suka taimaka masa wajen shirya wannan shu'umin taron koda da garwashin wutar kunnawa ne".
Anan nake jan hankalin matasa cewar kuji tsoron Allah ku kiyayi aikata irin wadannan miyagun bidi'o'in idan kun tashin yin aure. Sannan iyaye ma ya zama wajibi ku sanya ido ku rika yin nasiha ga 'ya'yanku game da irin wadannan haramtattun bidi'o'in, mutukar dai kuna so auren 'ya'yanku yayi albarka.
Sannan ku guji zurfafawa ko tsanantawa game da kayan lefe tunda babu shi acikin tsarin aure na musulunci. Al'adah ce ta kawoshi. Don haka arika sassautawa ana yin nasiha ga bangaren gidan maza cewar kada su matsa wa kansu, su kawo abinda ya sawwaka kawai. Kuma adena la'akari da cewar ai an kawo wa wance kaza-da-kaza, don me mu ba za'a kawo wa tamu 'diyar ba!!!
Muyi koyi da Manzon Allah ﷺ tunda auren nan dai sunnarsa ne. Mu guji aikata abinda zai kwashe albarkar auren.
WALLAHU A'ALAM
Allāh Ya Saka da alhairi
ReplyDeleteMuna matukar godiya
ReplyDelete