JARRABAWA KALA-KALA!!!!!
Tabbas munshiga cikin jarrabawa kala-kala daga wannan sai wannan.
Kuma ita jarrabawa sunnar Allah ce a bayan kasa. Allah ya fada a cikin alqur'ani cewa:
Aya ta farko:
1. ولنبلونكم بشيء من الخوف والجوع و نقص من الأموال والافس والثمرات. الخ.
2.انا خلقنا الانسان من نطفة امشاج نبتليه .
3.الذي خلق الموت والحيات لنبلوكم أيكم احسن عمل.
Duk wadannan ayoyi na tsamosu ne daga cikin
1. Suratul baqara
2. Suratul insaan
3.suratul mulki
Dukkan ayoyin su na magana na akan jarrabawan da Allah yake jarabtar bayinsa ne da su don ya Gane masu haquri da Kuma akasin haka.
Tabbas Allah ya jarrabemu da jarrabawa kala-kala daga wannan sai wannan, in wannan jarabawar tazo kafin ta futa sai wata ta shigo sabuwa. Wadannan jarabawowin su ne kamar haka:
1. Zuwa boko Haram
2. Kidnapping
3. Fatalwar yahudu (CORONA VIRUS)
4. Bandit
5. Fitinar mutuwa
6. Fitinar rayuwa
7. Tsadar kayan masarufi.
8. Ambaliyan ruwan kogi
9. Rashin tarbiyyar 'ya'ya mata da Samari.
10. Son 'ya'ya da dukiya.
11. Zaluncin masu mulki.
Wadannan abubuwa jarrabawa ce wadda Allah ya jarrabemu dasu a Nigeria, Amma sanadiyyar Munanan halayenmu. Allah ka bamu iKon gyarawa.
Al'umma su na cikin Wani Hali mummuna na tsadar rayuwa, mun tsunduma gonakai don yin noman abincin da zamuci kwatsam sai jarabawar ambaliya ta barke.
Ya Allah!!!! Ya Allah!!! Mun tuba mun dawo zuwa gareka Allah ka dauke mana wadannan abubuwa ka dawo mana da ni'imar da muka rasa.
Allah ka mayarwa waďanda ibtila'in ambaliya ya shafa da mafificin abinda suka rasa. Ya Allah ka kiyaye Gaba. Alfarmar alqur'ani.
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM