SHUGABAN MALAMAI NA JAHAR NIGER
HAFIZ ABU SUMAIYA MINNA, YA ZIYARCI SHEIKH JINGIR,
Jahar Niger ta ziyarar Shugaban Majalisar Malamai ta kasa da kasa na Kungiyar Izalatul Bid'ah wa'ikhamatis sunnah Fadilatul Ash-Shiekh Muhammad Sani Yahaya Jingir a Hedikwatar Kungiyar dake Jos. Ziyarar ta samu Jagorancin Shugaban Malamai ta Jahar Neja Sheikh Abubakar Abu Sumayya Usman tare da mataimakin shi na daya Dr. Idris Suleiman da mataimaki na biyu Sheikh Amb. Jibrila Abdullah da kuma shugaban gudanarwa ta Jahar Neja Alh. Haruna Musa da mataimakin shi na biyu Alh. Sa'adu Isah Koko da Sakateren gudanarwa Alh. Hussaini Ruwantsan da Mataimakin Shugaban Agaji Malam. Rabi'u Tunga da sauran muqarabai.
Bayane sun gabata inda shugaban majalisar malamai ta jahar Neja yayiwa Malam Barka da dawowa daga Kasa mai tsarki. Bayan ya gabatar da bayanan shi sai Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya gabatar da bayanan shi tare da yi mana ardu'oin alkhairi.
Muna godiya da tarba da akayi mana kuma muna rokon Allah ya karawa malam lafiya da rayuwa mai albarka amin.