GODIYA GA MALUMAN MU, SHUWAGABANNI, YAN SIYASAR MU DA DAUKACIN MAHALARTA A TARON KARAWA JUNA ILIMI DA KWAMITIN INTERNET MEDIA NA JIHAR PILATO JIBWIS NHQTRS JOS TA GABATAR
Assalamu alaikum
A Madadin kwamitin Internet Media na Jihar Pilato tana Mika godiyarta ga daukacin Jama'ar da Suka halarci budewa da Kuma rufe taron Karawa Juna ilimi da ta shirya a ranakun Asabar da Lahadi (10th-11th September,2022).
Na kan gaba Shine Shugaban Majalisar Mallamai na Kasa (Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir), Shugaban kungiya (Ash-Sheikh Nasir Abdulmuhyi).
Muna Mika godiya ta musammam ga babanmu Kuma Shugaban Majalisar Mallamai na Jihar Pilato Sheikh Dr. Hassan Abubakar Dikko Wanda bisa izininshi muka Sami Daman gudanar da wannan taro da daukacin Majalisar shi.
Har'ila yau Muna Mika godiyarmu ga Shugaban Internet Media na Kasa Ustaz Rabi'u Musa, Kwamishinan sufuri na Jihar Pilato Ustaz Muhammad Muhammad Abubakar, Alhaji Murtala Idris Malwa (Shugaban kwamitin wa'azin matasa na Kasa, Jibwis Nhqtrs Jos), Alh Ridwan Usman Abdullahi (Shugaban kwamitin wa'azin matasa na Jihar Pilato) da Kuma Alhaji Zakari Ambassador (Jibwis plateau state publicity Secretary).
Godiyarmu ga Maluman da suka gabatar da muqaloli na kan gaba Ustaz Yusuf Zakariyya, Ustaz Abdulra'uf Ahmad Getso da Kuma Ustaz Abdulkareem Ayuba.
Ba zamu kare ba sai munyi godiya ga Yan siyasar mu masu girma, na kan gaba Honourable Muhammad Shafi'u Yakub ( Dan takaran kujeran Sanata a Jam'iyyar NNPP) da Kuma kansilanmu matashi mai son Jama'a Honourable Sulaiman Tanimu (Sultan).
Ba zamu kare ba sai munyi godiya ga daukacin Excos na kwamitin Internet Media na Jihar Pilato da na kananan hukumomin Jihar Pilato bisa hadin kai da suka bamu don cimma nasara.
Muna godiya ga hukumar Makarantan Sunna Private School Unguwan Rimi Jos da bamu daman anfani da dakin taronsu.
Daga karshe Muna Rokon Allāh Ya Karawa rayuwar kowa cikin wadanda Muka ambata albarka ya Sanya shi cikin mizani Ranar gobe ya zamo sanadiyyar tsira garemu Baki daya.
GODIYA: IBRAHIM MAINA MUHAMMAD (SHUGABAN KWAMITIN INTERNET MEDIA, JIHAR PILATO)
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM