GWAMNATIN GOMBE TA ƘADDAMAR DA BADA TALLAFIN ABINCI GA MABUKATA.
Kwamiti Mai Mutane 30 Domin Raba Kayan Abinci A Jihar Gombe Ƙarƙashin Jagorancin Mai Kaltungo Engr. Sale Muhammad Umar 00N ta kaddamar da bada tallafin kayan abinci a fadin Jihar Gombe wanda ta fara bawa ƙaramar hukumar Gombe kamar yadda mai girma gwamnan jihar Gombe Alh Muhammadu Inuwa Yahaya ya bada umurnin rabawa mabukata.
Wannan rabo ya gudanane ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Mai Kaltungo Engr. Sale Muhammad Umar tare da membobin sa guda 30 don ganin saƙon ya isa ko'ina a faɗin jihar Gombe, a yau an fara gudanar da wannan rabo a ƙaramar hukumar Gombe tare da kafa kwamiti a kowace ƙaramar hukuma da kuma gundumomi 114 na jihar Gombe.
Bikin ƙaddamar da kayan abincin ya samu halartar membobin kwamiti 30 wanda ya haɗa da manyan malamai, sarakuna, fastoti da kuma kwamishinoni masu ruwa da tsaki acikin al'amuran Gwamnati da kuma al'umma da sauran shuwagabanni Jam'iyyar APC ne suka shaida kaddamarwa da kuma bada wannan Kayan abinci.
Cikin rabon, kowace ƙaramar hukuma zata samu Kayan abinci kamar yadda Sakataren kwamitin Alh Sa'ad Hassan ya zaiyano jadawalin buhun abinci kamar haka.
1 Ƙaramar Hukumar Akko Buhu - 12,636
2 Ƙaramar Hukumar Balanga Buhu - 6,858
3 Ƙaramar Hukumar Billiri Buhu - 5,454
4 Ƙaramar Hukumar Dukku Buhu - 7020
5 Ƙaramar Hukumar Kwami Buhu - 6,399
6 Ƙaramar Hukumar Kaltungo Buhu - 6,669
7 Ƙaramar Hukumar Gombe Buhu - 11,116
8 Ƙaramar Hukumar Funakaye Buhu- 9,966
9 Ƙaramar Hukumar Nafada Buhu - 3,537
10 Ƙaramar Hukumar Shomgom Buhu - 3,294
11 Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba Buhu- 10,827
Sannan Akwai Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu Sama da 26 Suma Sun samu Irin Wannan Kaso Na Kayan Abinci Kamar Yadda Akabi Sauran tsaruka Daban daban na raba wannan Kayan Abinci.
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM