GWAMNA ZULUM YA DAURA MATAKI NA KASO 75 CIKIN 100 NA ALƘAWARIN DA YA DAUKA DON KAMMALA MASALLACIN IZALA A BIU.
Cikin kokari da Mai girma Gwamnan jahar Borno Prof. Babagana Umara Zulum yakeyi tare da Mataimakinsa H.E Umar Usman Kadafur, don ganin sun kammala Masallacin Izala na daya dake kan titin Maiduguri Arewa da Shataletalen tsakiyar gari anan cikin garin Biu;
A yanzu haka an gama fentin ko ina da ko ina ciki da wajen masallaci dama azuzuwan dake saman masallaci,
Sannan an sanya wutan lantarki da fanka a cikin masallacin, ankuma hada dukkan wata na'ura na cikin masallacin, mu samman mai daukan sauti ya kai nesa,
A halinda ake ciki yanzu; abubuwan da suka rage basu da yawa wanda basu wuce kaso 25 cikin dari, muna kuma fatan gwamna zai gama cika alkawarin sa kamar yadda ya fara, Allah kuma ya saka musu da Alkhairi, Amin!
Zamu cigaba da kawo muku bayanai kan wannan aiki insha, Allah!
Muna rokon Allah daya sa a kammala wannan Masallaci lafiya kamar yadda aka fara ta lafiya, Amin!
Jibwis Biu Social Media
16th September, 2022M