ALHAMDULILLAH! ALƘAWARIN DA GWAMNA ZULUM YA DAUKA NA KAMMALA MASALLACIN DA AL'UMMA SUKA FARATA TANA GAB DA CIKA.
Cikin kokari da Mai girma Gwamnan jahar Borno Prof. Babagana Umara Zulum yakeyi tare da Mataimakinsa H.E Umar Usman Kadafur, don ganin sun kammala Masallacin Izala na daya dake kan titin Maiduguri Arewa da Shataletalen tsakiyar gari anan cikin garin Biu;
An kammala Filastan ko ina da ko ina, ciki da wajen Masallaci dama azuzuwa dake a saman masallacin, ankuma kara shafe masallacin da ceminti cikin wata sabuwar salo da shege na zamani wanda ake ce da ita (screeding), Masallaci tayu kyau ko ina da ko ina.
A halin da ake ciki yanzu masu filasta da screeding na kokarin nade tabarmansu, inda kuma Masu fenti na nan sunata jibge tabarminsu saura kiris su fara shinfideta.
Zamu cigaba da kawo muku bayanai kan wannan aiki insha, Allah!
Muna rokon Allah daya sa a kammala wannan Masallaci lafiya kamar yadda aka fara ta lafiya, Amin!
Jibwis Biu Social Media
12th September, 2022M
JIBWIS RADIO ONLINE
UKASHA KOKO ABU SHURAIM